Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta raba tallafin kuɗi da ya kai naira miliyan 33.8 ga iyalan ’yan sanda 50 da suka rasu yayin gudanar da aikinsu. An gudanar da bikin bayar da tallafin ne a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis 23 ga Oktoba, inda Kwamishinan ’Yan Sanda Bello Sani ya mika takardun ceki ga iyalan mamatan.
Sani ya bayyana cewa wannan tallafi na cikin shirin Group Life Assurance da IGP Family Welfare Scheme da aka ƙirƙira domin tallafawa iyalan jami’an da suka mutu a bakin aiki. Ya yabawa Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, bisa jajircewarsa wajen kula da walwalar jami’an sa da iyalansu, yana mai cewa wannan mataki ya kawo “farin ciki da sauƙin rayuwa” ga iyalan da abin ya shafa.
Kwamishinan ya shawarci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kuɗin wajen zuba jari mai amfani domin tabbatar da ci gaba da rayuwa ga ’ya’yan mamatan.
Wata mai suna Sonnen Mome, wacce ta karɓi tallafin a madadin sauran iyalan, ta gode wa IGP Egbetokun bisa wannan taimako, tana mai cewa hakan ya nuna cewa rundunar ’yan sanda ba ta manta da sadaukarwar jami’an da suka mutu ba, kuma tallafin zai taimaka wajen farfaɗo da rayuwar iyalan da abin ya shafa.
