Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa Jihar Filato domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da kuma fuskantar sabon ɓarkewar hare-haren rashin tsaro a jihar.
Matakin ya biyo bayan amincewar Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, na aika rundunar zuwa yankin.
A cewar sanarwar rundunar, dakarun da tuni suka isa Filato za su gudanar da ayyuka masu tsauri da farmaki kai tsaye domin murkushe ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar na da horo na musamman da kayan aiki na zamani da ake sa ran za su taimaka wajen inganta tsaro.
Yayin karɓar dakarun a hedikwatar 3 Division, Manjo Janar Folusho Oyinlola ya yaba da gaggawar jagoranci wajen samar da muhimman kayan aiki.
Ya ce goyon bayan zai taimaka wajen nasarar ayyukan tsaro, tare da roƙon al’ummar Filato kada su firgita da yawan motsin sojoji da kayan aikin soja.


