Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Rahotanni sun nuna cewa murabus ɗin ya biyo bayan takardar koke da mambobin hukumar suka aika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu suna neman a tsige shi.

Wani jami’in NAHCON ya ce shugaban ƙasar ne ya tilasta masa yin murabus sakamakon zarge-zargen da ke kansa.

Ya ce hukumar ta fuskanci cece-kuce da dama tun bayan naɗin Usman, kuma ana sa ran fadar shugaban ƙasa za ta sanar da wanda zai maye gurbinsa nan gaba.

Takardar koken, wadda mambobi 11 na kwamitin hukumar suka sanya wa hannu a ranar 19 ga Janairu 2026, ta zargi Usman da rashin gaskiya a harkokin kuɗi da karya dokokin kasafin kuɗi.

Haka kuma, an zarge shi da bayar da kwangilolin aikin hajji ba tare da bin ƙa’idoji ba, yayin da ake bincikensa a hukumar EFCC.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version