Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shigar da sabon haraji na kashi 15 cikin 100 (15%) kan duk wani man fetur da dizel da ake shigo da shi ƙasar nan. Wannan mataki na gwamnati na nufin ƙarfafa masana’antun tace mai na cikin gida da kuma daidaita farashin man fetur a kasuwa, duk da cewa zai iya jawo ƙarin farashi a gidajen mai.
A wata wasiƙa da aka rubuta ranar 21 ga Oktoba, 2025, Tinubu ya umurci Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Kula da Mai ta Tsakiya da Ƙasa (NMDPRA) da su fara aiwatar da harajin nan take. Shugaban FIRS, Zacch Adedeji, ne ya gabatar da wannan shawarwarin, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen ƙarfafa amfani da Naira wajen cinikin mai da kuma samar da daidaito tsakanin masu tace mai da ‘yan kasuwa.
Adedeji ya bayyana cewa, rashin daidaituwa tsakanin farashin man da ake tacewa a gida da na da ake shigo da shi ya jawo tashe-tashen farashi da rashin tsayayyiyar kasuwa, duk da cewa yanzu ana samun ci gaba a fannin tace man dizel da fetur a cikin gida. Ya kara da cewa, wannan haraji zai hana shigo da mai ba tare da biyan haraji ba, wanda ke iya cutar da masana’antun cikin gida.
Rahoton ya nuna cewa sabon harajin na iya ƙara farashin man fetur da karuwar N99.72 a kowace lita, inda hakan zai kai farashin mai a Legas zuwa kusan N964.72 kowace lita, wanda har yanzu ya fi ƙasashe da dama a yammacin Afirka arha. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnati ke ƙoƙarin rage dogaro da man shigo da ƙasashen waje, musamman bayan fara tace mai a matatar Dangote da wasu kanana a jihohin Edo, Rivers da Imo.
