Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen mako. Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar ’yan kasuwa da kuma gwamnatin Jihar Kano.
A cikin sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ba ga al’ummar kasuwancin Kano kaɗai ba, har ma da sassa da dama na Najeriya. Ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da jagorantar ƙungiyoyi masu alaƙa da kasuwanci a faɗin ƙasa.
Shugaban Ƙasan ya kuma tuna da gudunmawar da Bature Abdulaziz ya bayar wajen haɗa kan ’yan kasuwa, tare da goyon bayan da ya ba shi a zaɓen 2023. Haka kuma, ya jaddada rawar da marigayin ya taka wajen inganta haɗin kan ƙasa da kishin ƙasa ta hanyar ƙungiyar Patriotic Elders Network for Peace (PENP) da ya kafa.
