Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi ma’aikatan Abuja da ke yajin aiki da su koma bakin aiki daga ranar Laraba, 28 ga Janairu, ko kuma su fuskanci ladabtarwa. Ya ce duk wanda ya bijirewa umarnin kotu zai gamu da tsauraran matakai daga gwamnati.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja, jim kaɗan bayan kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin. Ya jaddada cewa doka dole ne ta yi aikinta.

Ministan ya ce gwamnatinsa ta riga ta gana da ƙungiyoyin ƙwadago tare da tattauna ƙorafe-ƙorafensu, inda aka magance mafi yawansu. Ya kara da cewa yajin aikin, wanda ya fara tun makon da ya gabata, ya jawo tsaiko da rufe ayyuka a manyan ofisoshin gwamnati kafin kotu ta ba da umarnin dakatar da shi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version