Jam’iyyar Labour Party (LP) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sanya hannu kan umarni na musamman (Executive Order) domin aiwatar da ’yancin kananan hukumomi, tana mai cewa jinkirin yin hakan na cin karo da hukuncin Kotun Koli da kuma muradun jama’ar ƙasa.
Jam’iyyar ta ce tun bayan hukuncin Kotun Koli na ranar 11 ga Yulin 2024 da ya ba da umarnin a rika tura kuɗin kananan hukumomi kai tsaye, gwamnonin jihohi na ci gaba da katsalandan a harkokin kuɗin kananan hukumomi, duk da amincewar Shugaba Tinubu kan buƙatar fitar da umarnin.
LP ta kuma zargi wasu gwamnonin, ciki har da na Jihar Ogun, da amfani da tsarin da ke raunana kananan hukumomi, tana mai kira ga Shugaban Ƙasa da ya umarci Ma’aikatar Kuɗi da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya su fara tura kuɗaɗe kai tsaye, tare da gargaɗin cewa ƙarin jinkiri na raina hukuncin Kotun Koli.
