A kalla mutum 17 ne suka rasa rayukansu a hare-hare daban-daban da ‘yan bindiga suka kai a jihohin Kaduna da Filato a ƙarshen mako. A Kaduna, ‘yan bindigar sun kutsa cikin garin Damakasuwa da ke cikin masarautar Chawai, ƙaramar hukumar Kauru, inda suka kashe mutum bakwai da jikkata wani. Shaidun gani da ido sun ce maharan sun zo da yamma, suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili, lamarin da ya sa mazauna yankin suka gudu cikin daji domin tsira da rayukansu.
Mai martaba sarkin Chawai, Alhaji Yahaya Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe mutane biyar a wurin, yayin da wasu biyu suka mutu daga baya saboda munanan raunuka. Ya ce an sake samun natsuwa bayan isowar jami’an tsaro, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankali. Wani matashin yankin, Barnabas Chawai, ya ce maharan sun far wa jama’a ne a lokacin da wasu ke bacci, wasu kuma har yanzu suna harkokinsu na yamma.
A jihar Filato kuwa, an tabbatar da mutuwar mutum goma a hare-hare guda biyu da suka faru tsakanin Juma’a da Asabar. A cewar wani jagoran al’umma, Rwang Tengwon, maharan da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai farmaki a garin Kwi, ƙaramar hukumar Riyom, inda suka kashe mutum bakwai. Haka kuma an kashe mutum uku a garin Pushit, ƙaramar hukumar Mangu, kamar yadda ƙungiyar ci gaban Mwaghavul ta tabbatar a wata sanarwa.
Hukumomin ‘yan sanda a jihohin biyu ba su fitar da cikakken bayani ba har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton. Sai dai gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya tabbatar da matakan tsaro da suka haɗa da hana kiwon dare da jigilar shanu bayan ƙarfe 7 na yamma da kuma hana amfani da babura daga 7 na yamma zuwa 6 na safe, domin rage hare-haren da ke addabar jihar.
