Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wasu matasa biyu da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma karya gidaje a cikin birnin Bauchi. Mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Wakil, ya bayyana cewa an kama su ne bayan wani rahoto da aka samu daga ofishin ‘yan sanda na C’ Division, Bauchi, wanda ya kai ga gano masu laifin.

Wakil ya ce, a ranar 22 ga Oktoba 2025, wata mata mai suna Na’ima Saleh ta kai rahoto cewa wani saurayi mai suna Abdulmalik Ismail, dan shekara 19 daga unguwar Karofin Madaki, ya shiga gidanta da niyyar yi mata fashi da wuka. Ta yi ihu, lamarin da ya jawo hankalin makwabta suka kama wanda ake zargin.

Bincike ya gano cewa wayar salula da aka samu a hannun Abdulmalik an sace ta ne a baya daga hannun wata Sadiyya Kabir, mai shekara 30. Bayan tambaya, ya amsa laifinsa tare da bayyana abokin aikinsa, Abubakar Saleh, dan shekara 20 daga unguwar Doya, wanda daga bisani shi ma aka kama kuma ya amsa laifin.

Kakakin rundunar ya ce an kwato babur, wuka biyu, da wayar Redmi daga hannunsu, kuma an mika su ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) na jihar Bauchi domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version