Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ’yan ta’adda sun ƙone mutane huɗu da ransu a gidajensu a ƙauyen Gwargwabe da ke yankin Nahuce, Ƙaramar Hukumar Bungudu. Harin ya faru ne da yammacin Alhamis kafin sallar Magariba, inda aka kashe maza uku da mace ɗaya tare da lalata gidaje, rumbunan abinci da dabbobi.
Gwamna Dauda Lawal ya halarci sallar jana’iza da binnewa, inda ta bakin mataimakinsa Mani Malam Mummuni ya jaddada kudirin gwamnati na kawo ƙarshen ta’addanci. Ya bukaci al’umma su dauki lamarin a matsayin ƙaddara, tare da tabbatar da fara bincike kan jinkirin isowar jami’an tsaro bayan sanar da harin.
Gwamnati ta sanar da kafa sansanin soja a Gwargwabe domin daƙile hare-haren gaba, tare da rabawa iyalan wadanda abin ya shafa buhunan hatsi 100 da tallafin Naira miliyan 10. A cewar hukuma, harin ya biyo bayan ƙin biyan harajin da ’yan ta’addan suka kakaba wa al’umma, lamarin da ya kara adadin mutanen da aka kashe a yankin zuwa bakwai cikin kwanaki kaɗan.
