Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya karyata jita-jitar cewa ya ƙulla wata yarjejeniya da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan domin haɗa kai don kawar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a 2027. Mai magana da yawansa kuma Shugaban Obidient Movement na duniya, Dr. Yunusa Tanko, ne ya bayyana hakan a hira da jaridar The PUNCH.

Tanko ya ce Obi da Jonathan suna da kyakkyawar alaƙar aiki tun da dadewa, kuma ganawarsu ba ta da wani ɓoyayyen ma’ana illa tattaunawa kan yadda za a inganta harkokin ƙasa. Ya ce ko a lokacin da suka gana a Ghana, ba a tattauna komai game da yarjejeniya ko haɗin gwiwar siyasa ba. Ganawar da aka yi a Abuja ta haifar da jita-jita a kafafen sada zumunta kan yiwuwar yin haɗin gwiwa tsakanin manyan ‘yan adawa.

Obi, wanda ya bayyana Jonathan a matsayin “babba kuma jagora” lokacin ganawarsu a watan Satumba, na ci gaba da gudanar da ganawa da shugabanni daban-daban a fadin ƙasar. Wannan mataki ana kallonsa a matsayin shiri na farko-farko na neman shugabanci a 2027, yayin da ake ci gaba da sukar gwamnatin Tinubu kan matsalolin tattalin arziki da siyasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version