Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wato Adamu Atiku Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa na Kwamishinan Ayyuka da Raya Makamashi a Jihar Adamawa. A wasiƙar da ya rubuta ranar 2 ga Maris 2026, ya gode wa gwamnan jihar bisa damar da aka ba shi na yin hidima tsawon wa’adi biyu.
Adamu ya yabawa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri kan amincewa da shi a muƙami mai muhimmanci, yana mai cewa wannan dama ta kasance abin alfahari. Ya kuma gode wa ma’aikatan ma’aikatar da al’ummar Jada bisa goyon baya da addu’o’i a lokacin da yake kan aiki.
Tsohon kwamishinan ya jaddada cewa murabus ɗinsa ba ya nufin ya daina hidimar jama’a ba, sai dai wata sabuwar hanya ce ta ci gaba da ba da gudummawa. Rahotanni sun ce yana da burin tsayawa takarar siyasa, yayin da ɗan uwansa Abba Atiku ke shirin neman kujerar majalisar wakilai.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version