Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin sanya hannu kan takardun hukuncin kisa ga duk wanda aka same shi da laifi a kisan Fatima Abubakar da ‘ya’yanta guda shida da aka yi kwanan nan.

Yusuf ya umarci Ofishin Lauyan Gwamnati da kwamishinan shari’a da su hanzarta gurfanar da wadanda ake tuhuma kan kisan don ganin adalci ya tabbata. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyara ta ta’aziyya a gidan iyalan wadanda aka kashe a Dorayi Chiranchi, inda ya yi ta’aziyya tare da nuna bakin ciki kan wannan mummunan kisa da ya girgiza jihar.

A matsayin tallafi ga wanda ya rasa dukan iyalinsa, gwamna ya amince da tura shi aikin Hajj da Umrah na 2026, samar masa da sabon gida, da kuma tallafawa wajen sake aure idan ya samu abokin rayuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version