Manjo janar Warra Idris, kwamandan Operation Fansan Yamma, ya tabbatar da mutuwar Aminu Kanawa, mataimakin shugaban kungiyar ta’addanci karkashin Bello Turji, sannan ya ce kwanakin shugaba Turji sun kusa karewa a Arewa maso Yamma. Idris ya bayyana cewa Turji da wasu manyan ‘yan ta’adda suna cikin rudani da firgici saboda yawaitar dabarun leken asiri da sojoji ke amfani da su wajen bibiyar su.

Kwamandan ya musanta zargin cewa Turji yana da iko a wasu garuruwa ko karamar hukuma, inda ya ce ‘yan ta’addan ba sa zama a wuri guda; suna yawo ne kawai don kashe fararen hula kafin su gudu. Ya kara da cewa Operation Fansan Yamma tana ci gaba da bibiyar Turji da wasu ‘yan tawagar sa kamar Gwaskadan Garemi, Ado Alero da Dogojide, tare da amfani da bayanai daga fadin kasar da makwabta wajen dakile su.

Idris ya ce a baya-bayan nan an cafke wasu masu samar da kayan aiki ga ‘yan ta’addan, inda ake ci gaba da bincike kan su. Haka nan Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da Jamhuriyar Nijar da Benin domin hana ‘yan ta’addan shiga kasar ba bisa ka’ida ba. Ya yi kira ga ‘yan jarida da su taimaka wajen yaki da labaran karya da ke kawo tarnaki ga yaki da ta’addanci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version