African Union ta yi Allah-wadai da hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara da suka yi sanadin mutuwar fararen hula sama da 50 tare da sace mata da yara. Shugaban hukumar ƙungiyar, Mahmoud Ali Youssouf, ya bayyana harin a matsayin take hakkin bil’adama da barazana ga zaman lafiya.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ƙauyen Dutsin Dan Ajiya da ke ƙaramar hukumar Anka, inda ‘yan bindiga sama da 150 suka kai farmaki a kan babura. Sun rufe hanyoyin shiga da fita, suka riƙa harbi, sannan suka ƙone gidaje, inda harin ya ɗauki sa’o’i tun daga daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a.

Ƙungiyar ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu tare da nuna goyon baya ga Najeriya, tana mai kira da a saki mutanen da aka sace ba tare da sharaɗi ba. Har ila yau, ta buƙaci ƙarin haɗin gwiwar tsaro domin kare jama’a, yayin da har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version