Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi kira ga masu hannu da shuni su taimaka wajen ciyar da mabukata a watan Ramadan. Ya yi wannan kira ne yayin ziyarar da ya kai wasu cibiyoyin da gwamnatinsa ke rabon abincin buɗe-baki ga masu azumi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na ciyar da aƙalla mutane 34,000 a kullum, inda ya ziyarci cibiyoyi a titin Clapperton, Lodge Road, Gidan Dallatu, asibitin ƙwararru da Madunka. Ya yaba da ingancin abincin da ake rabawa, yana mai cewa ya gamsu da yadda ake gudanar da shirin a bana.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware naira biliyan ɗaya domin shirin ciyarwar azumin bana. Gwamnan ya jaddada aniyar ci gaba da bai wa shirin muhimmanci, tare da yabawa masu aikin ciyarwar kan ƙoƙarin da suke yi wajen tallafa wa marasa ƙarfi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version