Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa ba a samu ko da lamari guda na lalata bututun mai ba a yankin Niger Delta a duk tsawon shekarar 2025. Babban Kwamandan Runduna ta 6, Manjo Janar Emmanuel Emekah, ne ya bayyana haka a ranar 20 ga Janairu, 2026 a Port Harcourt yayin rangadin manema labarai.

Emekah ya ce an samu wannan nasara ne ta hanyar ayyukan soji masu ɗorewa, sintiri bisa bayanan sirri, haɗin gwiwa da al’umma, da kuma aiki tare da sauran hukumomin tsaro. Ya ƙara da cewa tun daga hawansa muƙami a Janairu 2025, babu kamfanin mai da ya kai rahoton lalata bututu sakamakon ɓarna a yankin da rundunar ke kula da shi.

Ya bayyana cewa ingantaccen tsaro ya taimaka wajen ƙara yawan danyen man da Nijeriya ke samarwa zuwa kusan ganguna miliyan 2.2 a rana zuwa ƙarshen 2025, inda ya ce yawancin zubewar mai da ake samu na faruwa ne sakamakon tsofaffin bututu, ba wai lalatawa ba. Rundunar ta kuma jaddada ci gaba da yaƙi da haramtacciyar tace mai, tare da kiran hadin kan al’umma da kafafen watsa labarai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron yankin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version