’Yan sanda sun gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a gaban Kotun Majistri ta 53 da ke Normansland, Kano, kan zargin harƙallar filayen gwamnati da na al’umma. An gudanar da zaman kotun ne ranar Talata, 20 ga Janairu, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti.
A yayin zaman kotun, lauyan Sheikh Makwarari ya bayyana cewa ba su shirya gabatar da shi ba, yana mai nuna wa kotun cewa akwai wata shari’a makamanciya da ke gaban wata babbar kotu. Wannan ya sa lauyoyi suka roki kotu ta ba su lokaci kafin a ci gaba da gurfanar da wanda ake zargin.
Mai gabatar da kara, Barista Nura, ya bayyana wa kotun cewa an kawo shari’ar tun ranar 18 ga Nuwamba, amma daga baya ’yan sanda suka mayar da takardun zuwa ma’aikatar shari’a domin neman shawara kan ko akwai hujjojin laifi da za a gurfanar da Sheikh Makwarari ko a sallame shi.
Bayan sauraron bangarorin biyu, kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar Laraba, 21 ga Janairu 2026, domin ci gaba da gurfanar da wanda ake zargin tare da bayar da belinsa bisa wasu sharaɗi.
