Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa jam’iyyar APC za ta mara masa baya domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027. Ganduje ya faɗi hakan ne a Kano yayin taron maraba da gwamnan da ya koma APC.
Ganduje ya bayyana dawowar Yusuf APC a matsayin tarihi kuma mai amfani ga jam’iyyar da jihar Kano, yana mai cewa duk masu neman takara a jam’iyyar sun amince su yi aiki tare da shi. Ya ce dawowar gwamnan tamkar komawa gida ne, ganin cewa ya kasance cikin APC tun farkon kafuwarta.
Tsohon gwamnan Kano ya kuma ce, bisa tsarin APC, duk gwamna mai ci shi ne jagoran jam’iyya a jiharsa, don haka Abba Kabir Yusuf yanzu shi ne jagoran APC a Kano. Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta yi aiki tare da gwamnan ba tare da wariya ba, tare da hasashen nasara a zaɓuka masu zuwa.


