Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Ibrahim Umar, ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Umar ya sanar da murabus ɗin ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa gwamnan, wadda aka fitar ga manema labarai a daren Litinin.
A cikin wasiƙar, ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga tangardar da ta shiga tsakanin gwamnan da jagoransa na siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Ya ce duk da wahalar yanke shawarar, ya ga dacewar barin mukamin domin kare muradun jihar da kuma tafiyar da gwamnati cikin kwanciyar hankali.
Murabus ɗin nasa ya ƙara yawan kwamishinonin da suka ajiye aiki zuwa huɗu tun bayan sauyin siyasar da ya faru a Kano. Sauran sun haɗa da Kwamishinan Ayyukan Jin-ƙai Adamu Aliyu Kibiya, Kwamishinan Wasanni Mustapha Rabi’u Kwankwaso, da Yusuf Kofar Mata, yayin da Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar, Alhaji Rabi’u Saminu Danbappa, shima ya yi murabus.


