Ɗan fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya koma Najeriya a jiya Litinin bayan shafe kusan shekaru biyar yana gudun hijira a Jamhuriyar Benin. Komawarsa na zuwa ne bayan dogon lokaci da ya bar ƙasar sakamakon matsalolin tsaro.

Lamarin ya biyo bayan samamen da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kai masa a gidansa da ke Ibadan a shekarar 2021, wanda ya tilasta masa tserewa daga Najeriya. Tun daga wannan lokaci, Igboho ke zaune a ƙasashen waje ba tare da komawa gida ba.

Rahotanni sun ce ya samu damar dawowa ne sakamakon afuwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa, inda aka cire sunansa daga jerin mutanen da hukumomi ke nema. Sai dai har yanzu gwamnati ba ta bayyana cikakkun sharuddan afuwar da aka ba shi ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version