Wani ɗan kunar bakin wake da ake zargin na Boko Haram ne ya kai hari da mota cike da bama-bamai kan jerin gwanon sojoji a yankin Timbuktu na Jihar Borno a ranar Talata. Harin ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar, tare da jikkata wasu da ba a bayyana adadinsu ba.

 

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su akwai Manjo biyu da wani Laftanar. Harin ya lalata motocin sulke da kayan aikin sojoji da ake amfani da su wajen ayyukan yaƙi da ’yan ta’addanci.

 

Rahotanni sun ce sojojin suna dawowa ne daga wani aikin share sansanonin ’yan ta’adda da suka samu nasara kafin harin ya auku. An kai gawarwakin sojojin zuwa Maiduguri, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti, inda rundunar ta ce aikin tsaro a yankin na ci gaba duk da wannan hari.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version