Mazauna yankin Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara sun tsere zuwa makwabciyar jihar Niger bayan wani mummunan harin ta’addanci da ya yi ajalin fiye da mutum 176 a cikin mako. Harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da ruɗani.

Rahotanni sun ce harin ya fara ne da yammacin Talata zuwa safiyar Laraba, lamarin da ya tilasta wa iyalai barin gidajensu ba tare da kayan su ba. Wani bidiyo da ya bazu ya nuna mutanen da suka tsere sun taru a garin Wawa na jihar Niger, inda ake ganin mata da yara cikin gajiya.

Mai taimaka wa shugaban ƙaramar hukumar Kaiama, ZulQharnain Musa, ya tabbatar da cewa an kwashe yankin Woro gaba ɗaya. Ya ce an tura sojoji zuwa yankin bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, amma duk da haka mazauna yankin na ci gaba da jin tsoron komawa gidajensu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version