Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya buƙaci Majalisar Dokokin Najeriya da ta gaggauta amincewa da sauye-sauyen dokokin zaɓe da hukumar ta gabatar, domin tabbatar da ingantaccen shiri kafin babban zaɓe na gaba.

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin wata ganawa da tawagar sa ido kan zaɓe ta Tarayyar Turai (EU) ƙarƙashin jagorancin Barry Andrews, wanda ya jagoranci tawagar sa ido a babban zaɓen 2023.

A farkon shekarar nan, hukumar INEC ta mika jerin sauye-sauyen doka ga Majalisar Dokoki, wanda ya haɗa da:

Zaɓen wuri (Early Voting)

Zaɓen mazauna ƙasashen waje (Diaspora Voting)

Gyara amfani da katin zaɓe na dindindin

Bai wa INEC damar naɗa shugabannin zaɓe na jihohi

Samar da hukumomin sasanta rikicin zaɓe

Yakubu ya bayyana cewa amincewa da waɗannan sauye-sauyen da wuri zai bai wa hukumar damar tsara shirye-shiryen zaɓe cikin nasara kafin lokacin gudanar da babban zaɓe na gaba.

Ya ƙara da cewa INEC ta yi nazari sosai kan dukkan shawarwari takwas da tawagar sa ido ta EU ta bayar a rahotonsu na zaɓen 2023. A cewarsa, hukumar ta riga ta ɗauki matakai kan shawarwarin da ke buƙatar sauye-sauyen cikin gida, tare da ci gaba da aiki da sauran bangarori kan waɗanda suka shafi doka da tsarin mulki.

“Hukumar tana jiran kammala nazarin sauye-sauyen doka da Majalisar Dokoki ke yi, domin a aiwatar da su cikin lokaci,” in ji shi.

Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa shawarwarin EU da na sauran masu sa ido kan zaɓe suna daga cikin muhimman abubuwan da aka yi la’akari da su yayin nazarin bayan zaɓen 2023.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version