Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, ta ayyana ranar 20 ga Fabrairu, 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gaba. Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.

A cewarsa, za a gudanar da zaɓukan Majalisar Tarayya a ranar guda, wato 20 ga Fabrairu, yayin da zaɓukan gwamna da na majalisun jihohi za su gudana a ranar 6 ga Maris, 2027. Shugaban ya tabbatar da cewa hukumar ta kammala shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da sahihin zaɓe.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan kasafin kuɗin da hukumar ke nema domin shirya babban zaɓen 2027, wanda ya kai kusan Naira tiriliyan ɗaya. Hakan ya jawo muhawara a tsakanin ’yan majalisa da masu ruwa da tsaki kan yadda za a samar da isasshen kuɗi cikin lokaci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version