Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya da aka kafa domin sasanta sabanin da ke tsakanin Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe, zai gana ranar Litinin.
Ana sa ran kammala daidaita kudirin cikin mako guda kafin a miƙa shi ga Shugaba Bola Tinubu domin rattaba hannu.
Sabanin ya fi karkata kan batun amfani da fasaha wajen tattarawa da tura sakamakon zaɓe ta na’ura, musamman batun watsa sakamako kai tsaye zuwa IReV.
Majalisar Wakilai ta amince da watsa sakamako kai tsaye, yayin da Majalisar Dattawa ta tanadi cewa idan fasaha ta gaza, a koma ga tattarawa ta hannu.
Sanata Seriake Dickson ya buƙaci a rungumi sigar da Majalisar Wakilai ta amince da ita, yana mai cewa hakan zai ƙara yarda da tsarin zaɓe kafin 2027.
Haka kuma, tsohon shugaban NBA, Olisa Agbakoba, ya yi kira da a tabbatar da watsa sakamako kai tsaye a cikin doka, yana mai cewa hakan ne zai tabbatar da gaskiya da amincin zaɓe a ƙasa.



