Manyan jam’iyyun adawa ciki har da ADC, Labour Party da NNPP sun nuna damuwa kan jinkiri da rashin gaggawa daga Majalisar Tarayya wajen gyara Dokar Zaɓe gabanin zaɓen 2027. Sun ce wannan jinkiri na iya lalata sahihanci da amincewar jama’a ga zaɓen, musamman ganin yadda Majalisar Dattawa ke tafiyar da aikin gyaran dokar.

Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin wucin-gadi na mutum bakwai domin nazari da daidaita kudurorin gyaran dokar, karkashin jagorancin Sanata Niyi Adegbonmire. Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya ce kwamitin zai warware matsalolin da suka rage a tsarin gyaran dokar, bayan zaman sirri da ’yan majalisa suka yi kan kudirin.

Sai dai jam’iyyun adawa sun nuna shakku kan sahihancin kudirin, inda NNPP da Labour Party suka zargi ’yan majalisa da jan kafa don kare muradunsu. ADC ta yi gargadin cewa ci gaba da jinkiri ko raunana muhimman gyare-gyare kamar amfani da BVAS da tura sakamakon zaɓe ta lantarki na iya barazana ga sahihancin zaɓen 2027 baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version