Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce ya fi dacewa mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi murabus idan ba zai mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya ba. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Muhasa da ke Kano.
Waiya ya yi wannan jawabi ne a kan rahotannin da ke cewa mataimakin gwamnan na ci gaba da biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso duk da sauya sheƙar Gwamna Abba zuwa APC. Ya ce rashin jituwa a cikin gwamnati na iya kawo tangarda ga shugabanci, yana mai cewa gwamnati na buƙatar haɗin kai da manufa ɗaya domin cimma nasara.
Ya kuma yi nuni da cewa siyasar Kano na cike da gasa, inda mutane da dama ke da burin zama gwamna. Waiya ya ce idan muradin siyasa ya fara karo da alƙiblar gwamnati, mafita ita ce murabus, amma ya jaddada cewa shawarar ƙarshe tana hannun mataimakin gwamnan, yayin da gwamnati ke ci gaba da mayar da hankali kan ci gaban Kano.
