Shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya shigar da ƙara a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa. An yanke hukuncin ne bisa zargin aikata laifukan ta’addanci.

Alƙali James Omotosho ya yanke hukuncin a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, bayan ya same Kanu da laifi a dukkan tuhume-tuhume guda bakwai da gwamnati ta gabatar. Kotun ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 20 bisa kasancewa jagora a ƙungiyar da aka ayyana a matsayin ta’addanci, da kuma ƙarin shekaru biyar kan shigo da na’urar rediyo ba bisa ƙa’ida ba.

A cikin ƙarar da ya shigar, Kanu ya ce hukuncin ya ƙunshi kurakurai masu yawa. Ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke dukkan hukuncin da aka yanke masa, tare da buƙatar a sake shi gaba ɗaya daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version