Fitaccen mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya yi watsi da bullar sabbin jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027. Ya bayyana hakan a matsayin sake jujjuya tsoffin matsalolin siyasar Najeriya da sunaye kawai, ba tare da canji na gaske ba.

Sowore ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro da ya haɗa ’yan gwagwarmaya, ’yan jarida, lauyoyi da ƙungiyoyin farar hula. Ya ce yawancin ’yan siyasar da ke fitowa a matsayin sabbi su ne waɗanda suka rike muƙamai a gwamnatocin baya, yana mai cewa irin wannan dabarace ta yaudarar jama’a.

Ya kuma ce gwagwarmayar farar hula ta taimaka wajen rage danniya da samar da sauye-sauye, ciki har da ƙarin walwala a hukumomin tsaro da ɗaga darajar jami’an ’yan sanda da dama. Sowore ya jaddada cewa dole matasa su shiga siyasa kai tsaye, yana mai cewa shekarar 2026 muhimmiya ce wajen karɓe iko daga hannun waɗanda ba su iya tafiyar da shi yadda ya kamata ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version