Rundunar sojojin Operation HADIN KAI ta sanar da hallaka wani babban kwamandan ISWAP mai suna Julaibib a Jihar Borno. Hakan ya faru ne a ranar 30 ga Janairu 2026, bayan musayar wuta a yankin Kimba da ke karamar hukumar Damboa, inda aka ce mutuwar tasa ta jefa ’yan ta’addan yankin cikin rudani.

A cewar sanarwar rundunar, sojoji tare da hadin gwiwar Civilian JTF sun kuma hallaka wasu ’yan ta’adda uku a wani kwanton bauna tsakanin Ngazalgana da Lamusheri, inda suka kwato bindigogin AK-47 guda biyu. Haka kuma, a wani farmaki a Tsokorok da ke Gwoza, an kashe wani dan ta’adda tare da kwato babura biyu ba tare da asarar rai a bangaren sojoji ba.

Rundunar ta ce an samu nasarori makamantan haka a Adamawa, inda aka dakile yunkurin fashi da makami da kuma ceto wata mata da aka sace, sojoji sun jaddada kudirinsu na kare rayuka da dukiyoyi, tare da ci gaba da lalata cibiyoyin ’yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version