Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar soji zuwa sassan jihar Kwara, bayan mummunan harin da ya faru a ƙaramar hukumar Kaiama. Harin ya yi sanadiyyar kisan gomman mutane a yankin.
A wata sanarwa da kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar a daren Laraba, Tinubu ya naɗa kwamandan da zai jagoranci rundunar. Rundunar za ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya mai suna Operation Savanna Shield a jihar Kwara.
Matakin ya biyo bayan harin da aka kai ƙauyen Woro, inda aka tattara gawarwaki 78 a cewar rahotanni. Ɗan majalisar jihar Kwara, Hon. Sa’idu Baba Ahmed, ya shaida cewa sun yi jana’izar sama da 70, yana mai cewa an ga mutum 78, yayin da wasu aka ƙone a gidajensu, kuma maharan sun tafi da mata 38.
