Wasu ’yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari kasuwar shanu ta Kasuwar Daji da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara, inda suka sace shanu sama da 500. Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Najeriya a jihar, Aminu Garba, ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Garba ya bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun dade suna faruwa tsawon fiye da shekaru huɗu, inda ’yan bindigar ke shiga kasuwa da ƙauyukan da ke kewaye da ita tun da rana. Ya ce shanun da aka sace an tattara su ne daga kasuwanni daban-daban, ciki har da waɗanda aka shigo da su daga Jamhuriyar Nijar.
Wani daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Umar Mohammad, ya ce ’yan bindigar sun haura 100 kuma sun tsere da shanun zuwa yankin yammacin ƙauyen da ke kusa da daji. Ya ƙara da cewa an samu dawo da kusan shanu 60, yayin da rahotanni suka nuna cewa jami’an tsaro da ke kusa da kasuwar ba su kai ɗaukin gaggawa ba sai bayan ’yan bindigar sun tsere.
