Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano, Alhaji Sarki Aliyu Daneji, ya rasu. Rasuwar tasa ta zo ne a cikin yanayi mai tayar da hankali, inda aka sanar da mutuwarsa mintuna kaɗan bayan rasuwar wani ɗan majalisar jiha.
Tun da farko dai, an tabbatar da rasuwar Hon. Aminu Sa’adu, ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Ungoggo, lamarin da ya jefa al’ummar Kano cikin jimami da alhini.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya tabbatar da rasuwar tasu a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, da yammacin Laraba 24 ga Disamba, 2025.
