Gwamnatin Kano ta ci gaba da rushe gine-ginen da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a cikin birnin Kano, a wani mataki na tabbatar da bin dokokin tsara birane. An gudanar da sabon aikin rusau din ne a yankin Sharada Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale Local.
Aikin rushewar ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar ƙasa da tsara birane, Abduljabbar Muhammad Umar, bayan rahotannin cewa wasu mutane sun haɗa kai domin gina shaguna a wajen da mallakin Federal Housing Authority ne.
Kwamishinan ya ce filin an ware shi ne domin wuraren shakatawa, ba don kasuwanci ba, yana mai jaddada cewa duk wani gini da za a yi a wurin dole ne ya bi ƙa’idojin Kano State Urban Planning and Development Authority, tare da gargadin cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar mataki kan duk wanda ya karya dokokin amfani da ƙasa.

