Babbar Kotun Jiha mai lamba 17 ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Abdu Mai Wada Abubakar, ta soke nasarar Abdullahi Basaf a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano. Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata 24 ga Maris, 2026, bayan doguwar shari’a da aka kwashe lokaci ana yi.
Kotun ta kuma ayyana Ali Musa Danmaliki (Hardworker) a matsayin halastaccen shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso. Haka zalika ta bayyana takardar shaidar cin zaɓe da aka bai wa Basaf daga hukumar zaɓe ta jihar Kano a matsayin haramtacciya.
Bugu da ƙari, kotun ta umarci hukumar zaɓe ta KANSIEC da ta gaggauta bai wa Ali Musa Danmaliki takardar shaidar cin zaɓe. Har ila yau, ta jaddada cewa dole ne gwamnatin jihar Kano ta bi wannan hukunci ba tare da ɓata lokaci ba.

