Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu da nan take. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis 26 ga Maris, 2026.
Sanarwar ta ce an umarci tsohon kwamishinan da ya mika ragamar ma’aikatar ga Daraktan Kasuwanci nan take. Gwamna Yusuf ya gode masa bisa ayyukan da ya yi a lokacin da yake kan mukamin.
Haka kuma, gwamnan ya yaba da gudunmawar Sagagi wajen ci gaban jihar, musamman a fannoni na siyasa, addini da kananan da matsakaitan sana’o’i. Ya kuma yi masa fatan alheri a gaba tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta ayyukan jama’a da shugabanci nagari.

