Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya miƙa murabus daga mukaminsa, a wani mataki da ta ce an ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a harkokin mulki.
Sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar ta bayyana cewa murabus ɗin na da nufin bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba. Haka kuma ta jaddada cewa wannan mataki ba yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi ba ne.
Ƙungiyar ta ce Mataimakin Gwamnan ya bayyana kansa a matsayin mai tsabtataccen tarihi a aikin gwamnati, kuma ya ɗauki wannan mataki ne domin kauce wa rikice-rikicen siyasa da ka iya kawo tsaiko ga tafiyar gwamnati da ci gaban jihar.

