Manyan shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ciki har da Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas, sun taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 74 a duniya. Haka kuma mataimakan shugabannin majalisar, Barau Jibrin da Benjamin Kalu, sun bayyana nasu saƙonnin yabo ga shugaban.
Akpabio ya bayyana Tinubu a matsayin jagora mai hangen nesa da jarumtaka, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ya fara sun fara haifar da ɗa mai ido. Shi ma Abbas ya ce shugaban ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da kuma jagorantar gyare-gyare masu amfani ga ƙasa, musamman ƙarƙashin manufar “Renewed Hope Agenda”.
A nasa ɓangaren, Kalu da Barau sun yabawa salon jagorancin Tinubu, suna mai cewa ya taimaka wajen daidaita alkiblar ƙasar zuwa cigaba. Sun kuma bayyana fatan samun ƙarin nasara da lafiya ga shugaban, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara masa baya wajen aiwatar da manufofinsa.

