Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga jam’iyyar ADC a hukumance. Ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar ne a ranar Litinin a Gidan Kwankwasiyya da ke Miller Road, Bompai a Kano.
Manyan jiga-jigan siyasa sun halarci taron, ciki har da shugaban ADC na ƙasa, David Mark; Aminu Waziri Tambuwal; Rotimi Amaechi; Peter Obi; Dino Melaye da John Odigie-Oyegun. Hakan na nuni da muhimmancin taron a fagen siyasar ƙasa.
Tun da farko Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, yana mai cewa matakin ya zama dole sakamakon sauye-sauyen siyasa da ke gudana. Ya gode wa shugabannin jam’iyyar da magoya bayansa, yana mai jaddada cewa za su ci gaba da aiki tare domin kyautata makomar ƙasar.

