Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da cafke wani da ake zargin ɗan bindiga ne a ƙaramar hukumar Kaiama, a wani mataki na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da laifuka a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce an kama matashin mai suna Mallami Abubakar mai shekaru 20 ne a ranar 1 ga Afrilu, 2026 da safe, yayin wani sintiri na haɗin gwiwa tsakanin ‘yan sanda, jami’an gandun daji da kuma ‘yan sa-kai a yankin Nanu. Ta ce binciken farko ya nuna yana da alaƙa da wasu masu aikata laifuka a ciki da wajen jihar.
Bincike ya nuna cewa wani da ake kira Babi ne ya gayyace shi daga jihar Kogi zuwa wani wuri ta yankin Baruten domin shiga wata ƙungiya da ake zargin tana da alaƙa da ISWAP/Lakurawa. Rundunar ta ce wanda ake zargin yana tsare, ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin, tare da kira ga jama’a da su rika bai wa jami’an tsaro bayanai cikin lokaci.

