Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tambuwal da Kebbe, Abdulsamad Ibrahim Dasuki, ya buƙaci gwamnonin Arewa su gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna hanyoyin inganta dangantaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Dasuki ya bayyana cewa kyautata alaƙar ƙasashen biyu na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro da ke ƙara kamari a yankunan da ke kan iyakar Najeriya da Nijar. Ya ce rashin tsaro ya yi ƙamari musamman a wasu sassan Jihar Sakkwato.
Da yake jawabi a Sakkwato, Dasuki ya kuma shawarci Gwamnan Jihar Sakkwato ya nemi amincewar gwamnatin tarayya domin kafa rundunar masu tsaron daji. Haka kuma ya bayyana goyon bayansa ga kafa ’yan sandan jihohi, tare da nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar ADC za ta yi tasiri a zaɓen 2027.

