Rukunin ƴan Najeriya na biyu sun dawo gida daga ƙasar Afirka ta Kudu bayan jinkirin da aka samu a shirin ƙwaso mutanen da suka nemi komawa gida sakamakon tashe-tashen hankula da suka shafi ƙin jinin baƙi a ƙasar.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar cewa kusan mutum 50 sun isa Najeriya da sanyin safiyar Alhamis. Ya kuma bayyana cewa sama da ƴan Najeriya 700 da suka yi rajistar shirin na ci gaba da jiran dawowarsu.
Tun da farko, fiye da mutum 260 sun dawo Legas a ranar 11 ga watan Yuni bayan sun nemi komawa gida da radin kansu. Haka kuma, jami’an Najeriya sun ce sama da mutum 1,000 ne suka nuna sha’awar dawowa bayan yaɗuwar hare-hare da zanga-zangar ƙin jinin baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu.

