Mamakon ruwan sama ya lalata gidaje sama da 20 tare da gonaki a yankin Darwat-Jol da ke Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato. Ambaliyar da ruwan ya haddasa ta tilasta wa mutane da dama barin gidajensu bayan ta mamaye yankin.
Wani mazaunin yankin, Malam Damba Dang, ya ce ruwan saman na daga cikin mafi ƙarfi da aka samu a yankin cikin ’yan shekarun nan. Ya bayyana cewa rashin ingantattun magudanan ruwa ne ya ƙara tsananta ambaliyar, wadda ta rusa gidaje tare da lalata kayan jama’a da gonaki.
Mazauna yankin sun ce lalacewar gonakin ta ƙara jefa manoma cikin mawuyacin hali. Sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato, hukumomin agajin gaggawa da sauran ƙungiyoyi da su kai musu ɗaukin gaggawa domin tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.

