Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce yana da ƙwarewa da salon shugabancin da za su ba shi damar haɗa kan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa. Ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
Obi ya musanta zargin cewa zai raba kan ƙasar idan ya zama shugaban ƙasa, yana mai cewa ayyukan da ya gudanar a baya sun nuna ƙudirinsa na haɗa kan ‘yan Najeriya. Ya ce ya kai ziyara tare da tallafa wa al’ummomin da rikice-rikice da iftila’i suka shafa a jihohin Arewa.
Ya ce ya bayar da gudummawa ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Borno, tare da taimakawa wajen haƙa rijiyoyin burtsatse da tallafa wa makarantu, asibitoci da sauran ayyukan ci gaba a jihohin Kano, Kaduna, Gombe, Bauchi da Sakkwato.
Obi ya jaddada cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen haɗa kan ƙasa, samar da zaman lafiya da bai wa kowane ɗan Najeriya dama iri ɗaya ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba. Haka kuma ya musanta zargin cewa ya taɓa yin kalaman wariya ga mutanen Arewa.

