Jam’iyyar PDP ta ɗora bayanan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a shafin hukumar zaɓe ta Nijeriya (INEC), a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ‘Pantamiyya Movement’ ta ce an kammala ɗora bayanan Pantami a shafin INEC ne a ranar 26 ga Yuli, 2026, bayan da ya zama ɗan takarar PDP ba tare da hamayya ba a ranar 26 ga Mayu.
A cewar ƙungiyar, sauran masu neman takarar ba su samu amincewar Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na PDP ba, sannan ba su karɓi takardar shaidar cancantarsu ba. Ta kuma ce INEC ta sanya ido kan tsarin zaɓen da aka gudanar bisa dokokin zaɓe da ƙa’idojin jam’iyyar.
Ƙungiyar ta ce Pantami na da gogewa wajen shugabanci, inda ta ambaci ayyukansa a matsayin tsohon Darakta Janar na NITDA da kuma tsohon minista. Ta kuma ce idan aka zaɓe shi gwamna, zai mayar da hankali kan ilimi, tattalin arzikin zamani, noma, masana’antu, tsaro, ƙarfafa matasa da inganta shugabanci mai adalci.

