Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce mutanen da ke aikata hare-hare da kashe-kashe a Jihar Plateau ba su da alaƙa da wata ƙabila ko addini.
Shettima ya yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗora laifin wasu masu aikata miyagun laifuka kan al’umma baki ɗaya ba, yana mai cewa hakan na ƙara rura wutar rikici maimakon samar da mafita.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin cika shekaru 80 da haihuwa tare da ƙaddamar da littafin tarihin tsohon Gwamnan Plateau, Sanata Jonah Jang, a Jos. Ya kuma yi kira ga matasa da su yi watsi da ƙiyayya, su rungumi zaman lafiya, yafiya da sulhu.
Shettima ya ce masu ta’addanci da kashe-kashen da ake gani ba su da izini daga kowace al’umma, ƙabila ko addini. Ya buƙaci dattawan Plateau su ci gaba da ilmantar da matasa kan illar ƙiyayya da ramuwar gayya, tare da jagorantar su zuwa hanyar yafiya da haɗin kai.

