Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙayyade Naira miliyan 7,672,822 a matsayin kuɗin kujerar Hajjin shekarar 2027. Daraktan-Janar na hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan.
Alhaji Labbo ya ce maniyyatan da suka riga suka biya Naira miliyan 7.5 za su ƙara biyan Naira 172,822 domin cika kuɗin kujerar Hajjin.
Ya bayyana cewa 18 ga Satumba 2026 ce ranar ƙarshe da aka sanya wa maniyyatan jihar domin kammala biyan kuɗin. Ya kuma umarci jami’an hukumar da ke yankuna daban-daban da su ƙara wayar da kan alhazai kan buƙatar kammala shirye-shiryen tafiyar.
Daraktan-Janar ɗin ya yaba wa jami’an hukumar kan ƙoƙarinsu, tare da gode wa Gwamnan Jigawa, Malam Umar A. Namadi, bisa tallafin da yake bai wa hukumar. Hukumar ta buƙaci maniyyatan da abin ya shafa su gaggauta biyan sauran kuɗin kafin cikar wa’adin.

