Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce da Gwamnatin Tarayya na son kwace zaɓen gwamnan Osun na 15 ga Agusta, da babu abin da zai hana ta. Sai dai ya ce zaɓen ya kasance mai matukar zafi, inda kowanne ɗan takara zai iya yin nasara.
Fayose ya bayyana hakan ne a wata hira da TVC News, yana mai cewa ya shafe lokaci a Osun kafin da lokacin zaɓen, yana zagayawa kasuwanni da al’ummomi domin jin ra’ayoyin jama’a. Ya ce abin da ya gani ya nuna cewa ba za a iya hasashen wanda zai yi nasara cikin sauƙi ba.
Ya ce rabon ƙuri’un ne ya taimaka wajen tabbatar da nasarar Gwamna Ademola Adeleke, musamman a Ede, wadda ake ɗauka a matsayin tungar siyasar iyalan Adeleke. Fayose ya ce daga cikin tazarar ƙuri’u kusan 66,000 da Adeleke ya samu, kimanin 46,000 daga Ede ne.
Fayose ya kuma yi Allah wadai da tashin hankalin da ya faru yayin zaɓen, yana mai cewa bai kamata hakan ya faru ba. Ya taya Adeleke murna tare da kira gare shi da ya yi amfani da nasarar wajen haɗa kan al’ummar Osun, ya kuma yi sulhu da dukkan masu ruwa da tsaki ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba.

