Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka (FBI) ta bayyana bayanan da take da su kan Shugaba Bola Tinubu, matuƙar dokokin Amurka sun ba da damar yin hakan.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar. Atiku ya tambayi dalilin da ya sa FBI ke cewa bayyana wasu bayanai na iya jefa rayukan mutane cikin haɗari.
Atiku ya ce ’yan Najeriya na fama da matsalolin tsaro, tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi, lamarin da ya ce ke haddasa mutuwar mutane sakamakon hare-haren ’yan ta’adda, yunwa da rashin kuɗin magani.
Ya kuma soki manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur. Atiku ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, zai dawo da tallafin man fetur cikin tsari, tare da yin kira ga FBI da ta bayyana duk bayanan da doka ta ba da damar fitarwa ba tare da jefa masu bincike, majiyoyi ko ayyukan tsaro cikin haɗari ba.

